Matthew 5

Albarku

1Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa, 2sai ya fara koya musu yana cewa:

3“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,
gama mulkin sama nasu ne.
4Masu albarka ne waɗanda suke makoki,
gama za a yi musu taʼaziyya.
5Masu albarka ne waɗanda suke masu tawaliʼu,
gama za su gāji duniya.
6Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa saboda adalci,
gama za a ƙosar da su.
7Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,
gama za a nuna musu jinƙai.
8Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,
gama za su ga Allah.
9Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,
gama za a kira su ʼyaʼyan Allah.
10Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu saboda adalci,
gama mulkin sama nasu ne.
11“Masu albarka ne ku saʼad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku, saboda ni. 12Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa yana a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

Gishiri da kuma Haske

13“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.

14“Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. 15Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan alkuki, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. 16Haka ma, bari haskenku yǎ haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

Cikar Doka

17“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su. 18Gaskiya nake gaya muku, sai sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome. 19Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama. 20Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.

Kisankai

21“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;
Fit 20.13
kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’
22Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗanʼuwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗanʼuwansa ‘Raka,
Kalmar Aramayik ta reni
 ’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

23“Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗanʼuwanka yana riƙe da kai a zuci, 24sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗanʼuwanka; saʼan nan ka zo ka ba da baikonka.

25“Ka yi hanzari ka shirya alʼamura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yǎ miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. 26Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.

Zina

27“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
Fit 20.14
28Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, saʼan nan ya yi shaʼawarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.

Kashen Aure

31“An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yǎ ba ta takardar saki.’
M Sh 24.1
32Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

Rantsuwa

33“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam: ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yǎ zama fari ko baƙi ba. 37Bari ‘I’ naku yǎ zama ‘I’; ‘Aʼa’ naku kuma yǎ zama ‘Aʼa.’ Duk abin da ya wuce haka, to, daga wurin mugun nan ne.

Ramuwa

38“Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’
Fit 21.24; L Fir 24.20; M Sh 19.21
39Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma. 40In kuma wani yana so yǎ yi ƙararka yǎ ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma. 41In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu. 42Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.

Ƙauna don Abokan Gāba

43“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka,
L Fir 19.18
ka kuma ƙi abokin gābanka.’
44Amma ina gaya muku: Ku ƙaunaci abokan gābanku
Waɗansu rubuce rubucen hannun da ba su jima ba suna da abokan gāba, ku sa wa waɗanda suke laʼantarku albarka, ku yi wa waɗanda suke ƙinku alheri
kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku adduʼa,
45don ku zama ʼyaʼyan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47In kuwa kuna gai da ʼyanʼuwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48Ku fa zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

Copyright information for HauSRK